Jami’i a kungiyar ta Hamas Suhail al-Hindi ya mika godiyarsa ga jamhuriyar musulunci ta Iran saboda goyon bayan da take bai wa Falasdinawa a fuskoki mabanbanta.
Har ila yau al-Hindi ya yi wa kungiyar Hizbullah ta Lebanon godiya,musamman shahid sayyid Hassan Nasarallah wanda ya yi shahada akan hanyar Kudus.
Bugu da kari, al-Hindi ya mika jinjina ga kungiyar Ansarullah ta Yemen, da kuma kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Iraki saboda rawar da su ka taka wajen taya Falasdinawa fada da HKI.