Kungiyar Hamas ta bayyana cewa a halin yanzu batun tsagaita budewa juna wata a Gaza da kuma musayar fursinoni ba zai yu ba sai da takurawa HKI.
Kakakin kungiyar, Jihad Taha ne ya bayyana haka a hirar da ta hada shi da shafin labarai na ‘Arabi 21’ a yau Talata. Ya kuma kara da cewa kungiyar tana goyon bayan dukkan shawarorin da kasashe daban daban suka gabatar na tsagaita budewa juna wuta da musayar fursinoni a Gaza, daga ciki har da ta kasashen Katar da Masar a ranar 6 ga watan Mayun shekara ta 2024, amma gwamnatin HKI ce ta ki amincewa da su.
Taha ya kara da cewa HKI tana ci gaba da aikata kissan kiyashi a Gaza don tabbatar da cewa ba wata yarjeniyar zaman lafiya da musayar wutan da zata sami nasarar a aiwatar da ita. Daga karshe ya bayyana cewa a halin da ake ciki, ba abinda zai yi aiki, sai takurawa HKI kan amincewa da daya daga cikin shawarorin da aka gabatar na tsagaita wuta da kuma musayar fursinoni.
A halin yanzu dai kasashen Amurka, Masar da kuma Katar zasu sake haduwa a birnin Doha na kasar Katar ko kuma Alkahira na kasar Masar a ranar 15 ga watan Augustan da muke ciki don tattauna batun tsagaita wuta a yakin na Gaza. Sai dai ita Hamas tana ganin maimakon a bude sabuwar yarjeniya na tsagaita wuta, a dauko daya daga cikin na baya a aiwatar da ita.