Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta bada rahoton cewa sojojin HKI sun kashe akalla yara 16 tun farkon wannan shekara ta 2025 a yankin yamma da kogin Jordan.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ayed Abu Eqtaish, daraktan kungiyar ‘ The Defense for Children International’ a yankin yamma da kogin Jordan yana fadar haka. Ya kuma zargi manya manyan kasashen duniya da kyale gwamnatin HKI ta na aikata irin wadannan laifuka kan Falasdinawa a gaban idan kowa.
Eqtaish ya kara da cewa, rashin magana da kuma rashin takawa gwamnatin yahudawan birki ya na sa ta kara yawan kisan yara Falasdinawa a duk sanda ta ga dama.
Kafin haka wani rahoton MDD ya tabbatar da cewa idan ba’a ha na HKI da karfi ba, to ba za ta takaita kisan kiyanshi a Gaza kadai ba, zata fadadashi zuwa yankin yamma da kogin Jordan.
Sojojin HKI sun aikata laifukan yaki da kisan kiyashi a gaza na tsawon watanni 15, inda ta kashe falasdinawa fiye da 61,000 kafin a tsagaita wuta a ranar 19 ga watan Jenerun da ya gabata.