Kungiyar Hamas wacce take gwagwarmaya da HKI a kasar Falasdinu da aka mamaye, ta bayyana jawabin firai ministan HKI Benyamin Natanyahu a babban zauren MDD a juya Jumma’a yana cike da karyayyaki.
Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana ta ciwa abinda mutane suka ji a jawabin Natanyahu a jiya, wani abu ne wanda ya nuna cewa duniya tana cikin hatsari daga wannan mutum.
Kungiyar ta kara da cewa kashe falasdinawa da yunwa a Gaza wani abu ne wanda MDD ta tabbatar da hakan. Don haka batun amfani da yunwa a matsayin makami wanda natanyahu yake yi gaskiya ne kuma laifin yaki ne.
Jakadun kasashen duniya da dama a MDD sun fice daga babban zauren Majalisar a lokacinda Natanyahu yake jawabi.
Sami Abu Zuhri daya daga cikin shuwagabannin Hamas ya ce, dangane da maganar Natanyahu na dole ne sai kungiyar Hamas ta mika kai ta kuma mika makamata ga gwamnatinsa!, yace wannan Kalmar ta mika kai ga HKI baya cikin kamus na kungiyar.