Hamas ta tabbatar cewa “Shawarar da Netanyahu ya yanke na dakatar da shigar da kayan agajin da jin kai na kasashen duniya zuwa zirin Gaza, hakan na a matsayin laifin yaki da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni.”
Kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila lamba da ta dakatar da matakin da ta dauka na yunkurin halaka mutane fiye da miliyan 2, inda ta kara da cewa, bayanin Netanyahu dangane da tsawaita matakin farko wani yunkuri ne na kaucewa yarjejeniyar, da kuma kaucewa shiga tattaunawa a mataki na biyu.
Tun da farko a ranar Lahadin da ta gabata, Isra’ila ta sanar da dakatar da duk wani taimakon jin kai ga Gaza da kuma rufe hanyoyin shiga yankin, tana mai jaddada cewa “Isra’ila ba za ta amince da tsagaita wuta ba, ba tare da sakin dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su ba, kuma idan Hamas ta ci gaba da kin amincewa da hakan, to za a samu wani sakamako.
Hamas ta jaddada muhimmancin kashi na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta; duk da haka, “Isra’ila” ta sanar da cewa ta amince da shawarar Amurka na tsawaita wa’adin tsagaita bude wuta a halin yanzu har zuwa tsakiyar watan Afrilu, yayin da tattaunawar da aka yi a mataki na biyu ta kasa samar da sakamakon da ake bukata.