Rahotanni sun bayyana cewa bangarorin falasdinawa sun yi watsi da kudurin da aka kaddamar ga kwamitin sulhu na majalsar dinkin duniya na shirin aikewa da sojojin ketare zuwa yankin Gaza sun yi kira ga kasar Aljeriya da sauran mambobin da ba na dindin ba a kwamitin sulhu da su kalubalance shi.
Daftarin kudurin an tsara za’a kada kuri’a akan shi a yau litinin na yiyuwar akewa da dakarun kasashen waje 20,000 domin kulawa da iyakokin Gaza, da kuma bada huro ga yan sandan falasdinu .
A Sanarwar hadin guiwar dukkan bangarorin falasdinawan sun yi tir da wannan shiri, inda suka bayyana shi a matsayin wani sabon salo na kara mamaye yankin dama alummarsa, domin bada halacci ga zaman dakarun kasashen waje a yankin.
Mai Magana da yawun kungiyar Hamas Hazem Qaseem ya jadda cewa amincewa da daftarin kudurin da Amurka ta gabatar ba zai kawo zaman lafiya da daidaito ba a yankin Gaza, don haka ya bukaci kwamitin tsaro da ya kare musu hakkokinsu da kuma hana afkuwar yaki a yankin