Hamas: Babu gudu babu ja da baya game da gwagwarmaya da zalunci da mamayar Isra’ila

Babban kusa kuma mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas Khalil Al-Hayya, ya gabatar da jawabi game da cika shekara guda da kaddamar da farmakin

Babban kusa kuma mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas Khalil Al-Hayya, ya gabatar da jawabi game da cika shekara guda da kaddamar da farmakin guguwar Aqsa, inda ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya dangane da gwagwarmayar yaki da zaluncin Isra’ila a Falastinu, har sai sun ‘yantar da kasarsu daga mamayar yahudawa.

Babban Mamban a ofishin siyasa na kungiyar Hamas kuma shugaban ofishin hulda da kasashen Larabawa da na Musulmi a kungiyar Hamas, Khalil Al-Hayya, ya tabbatar da cewa tsallakawar ‘yan gwagwarmaya daga zirin Gaza zuwa cikin yankunan Falasdinawa da yahudawa suka mamaye a ranar 7 ga Oktoba, 2023 “ya wargaza tunanin ‘yan mamaya.

A cikin jawabin da ya gabatar a zagayowar ranar farko ta farmakin gudguwar Al-Aqsa,  Al-Hayya ya jaddada cewa tsayin daka a wannan rana ya haifar da babbar barazana ga gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila a matakin tsaro da na soja,” ta yadda hakan ya nuna gazawar bangarori daban-daban na tsarinta na soja da na tsaro, tare da dora shi akan asarar da ba a taba ganin irinta a tsakanin sojojin yahudawan ba.

Al-Hayya ya kara da cewa ta sakamakon kaddamar da wannan farmaki, Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta fahimci  cewa babu wata makoma ga wanzuwarta, kuma al’ummar Palastinu za su ci gaba da jihadi da tsayin daka, ko ba dade ko ba jima har sai sun kori ‘yan share wuri zauna daga kasarsu.

Al-Hayya ya kuma jinjinawa dukkanin sauran kungiyoyin gwagwarmayar falastinawa, da sauran kungiyoyin gwagwarmaya na Lebanon, Yemen, Iraki da kuma kasar Iran, wadanda suka taka gagarumar rawa wajen taimakon al’ummar Palastinu.

Kamar yadda ya jinjinawa manyan kwamnadojin gwagwarmaya na yankin da suka yi shahada, musamman Isma’il Haniyya da Sayyid Hassan Nasrallah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments