Hamas: An Cimma Yarjejeniyar Karshen Kan Dakatar Da Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Gaza

Kungiyar Hamas ta sanar da yarjejeniyar kawo karshen hare-haren wuce gona da irin gwamnatin mamayar Isra’ila kan Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar

Kungiyar Hamas ta sanar da yarjejeniyar kawo karshen hare-haren wuce gona da irin gwamnatin mamayar Isra’ila kan Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar a yau Alhamis cewa, ta cimma yarjejeniyar kawo karshen hare-haren da gwamnatin mamayar Isra’ila ke kai wa Gaza, da janyewar sojojin mamaya daga cikinta, da shigar da kayan agaji da ci gaba da musayar fursunoni.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Kungiyar Hamas ta tabbatar a cikin wata sanarwa a hukumance, bayan shafe tsawon lokaci ana gudanar da yakin kisan kare dangi a Gaza cewa ta cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin, da janyewar sojojin mamaya daga cikinta, da shigar da kayan agaji, da musayar fursunoni.

Ya yi nuni da cewa, hakan ya zo ne bayan tattaunawa mai wahalar gaske da aka yi tsakanin kungiyar da bangaren gwagwarmayar Falastinawa dangane da shawarar da shugaban Amurka Trump ya gabatar a birnin Sharm el-Sheikh, da nufin kawo karshen yakin neman shafe al’ummar Falastinu.

Kungiyar Hamas ta yi kira ga shugaban Amurka Donald Trump, da kasashen da suka amince da yarjejeniyar, da kuma bangarori daban-daban na kasashen Larabawa, da na Musulmi da na kasa da kasa da su tilasta wa gwamnatin mamayar Isra’ila aiwatar da ka’idojin yarjejeniyar da kuma hana ta kaucewa ko jinkirta aiwatar da abin da aka amince da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments