Gwmnatin Najeriya Ta Bayyana Kudirinta Na Bunkasa Alaka Da Iran

Gwamnatin Najeriya ta ce ta kuduri aniyar kara karfafa dangantakar da ke tsakaninta da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A cikin wata sanarwa da ta fitar

Gwamnatin Najeriya ta ce ta kuduri aniyar kara karfafa dangantakar da ke tsakaninta da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba don taya kasar Gabas ta Tsakiya murnar zagayowar ranar juyin juya halin Musulunci, Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce Najeriya na shirin ci gaba da huldar diflomasiyya da hadin gwiwa mai amfani ga dukkan bangarorin biyu.

Wannan bikin ya zo ne a daidai lokacin da ake cikin rikici tsakanin Tehran da Amurka.

A cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar Najeriya ta bayyana bikin a matsayin wani muhimmin lokaci na tarihi wanda ke nuna jajircewar Iran ga ‘yancin kai da ci gaban kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted