Gwamnonin jihohin kudu maso yammacin Najeriya sun bada sanarwan cewa lokaci yayi na kafa yansandan jihohi, har’ila yau da kuma karfafa kula da dazuzzukan kasar saboda magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto gwamnonin na fadar haka a jiya Litinin, bayan taron gwamnonin shiyar kudu maso yammacin kasar da aka gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Gwamnonin 6, sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aiko masu gadin dazuzzuka a shiyar kudu maso yammacin kasar, don tabbatar da tsaronsu. Har’ila yau gwamnonin jihohin guda shida ne zasu dauki nauyin kula da jami’an tsaron dazuzzukan.
Labarin ya kara da cewa shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ne ya karanta jawabin bayan taron gwamononin. Sauran gwamnonin dai sun hada da Dapo Abiodun na jihar Ogun, Biodun Oyebanji na jihar Ekiti, Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo, Ademola Adeleke na jihar Osun, wanda mataimakinsa , Yerima Kola Adewusi ya wakilta sai kuma gwamna mai masaukin baki Seyi Makinde na jihar Oyo.
Taron gwamnonin ya yabawa gwamnatin tarayyar kan kokarin da take yi na magance matsalolin tsaro a arewacin kasar, suna kuma gabatar da alhininsu gareta saboda abubuwan bakin ciki da suka faru a jihohin Kebbi, Naija da kuma Kwara na sace daliban makarantu da kuma kashe wasu malamansu.