Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ta Sake Aiwatar Da Kisan Kiyashi A Sansanin Falasdinawa Na Jabaliya

Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da

Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza

Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Tal al-Za’atar da ke gabashin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza.

A cewar majiyoyin yankin, gidan da aka kai harin na dangin Nasiyo ne, kuma yana dauke da ‘yan gudun hijira daga iyalai sama da biyar a cikinsa, inda harin ya turbude su a karkashin baraguzan gine-gine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments