Gwamnatin Yamen Tana Tsare Da Ma’aikatan MDD 50 Ta Kuma Kwace Kayakin Aikinsu

Gwamnatin kasar Yemen ta kama wasu ma’aikatan MDD a ranar Lahadi a cikin kasar a wani sumamen da Jami’an tsaron kasar suka yi kan sansaninsu,

Gwamnatin kasar Yemen ta kama wasu ma’aikatan MDD a ranar Lahadi a cikin kasar a wani sumamen da Jami’an tsaron kasar suka yi kan sansaninsu, inda suka kama ma’aikatan suka kuma kawace kayakin aikinsu.

Shafin yada labarai na Yanar Gizo ArabNews na kasar Saudiya sun ya nakalto kamfanin dillancin labaran Associated Press yana cewa a jiya Lahadi ne jami’an tsaron yemen suka kama yemenawa 11 da kuma yan kasashen waje 15  a wani wurin aikinsu a unguwar Hada na birnin San’a babban birnin kasar.

Labarin ya kara da cewa sun sallami 11 daga cikinsu bayan tambayoyi masu yawa. Jean Alam kakakin MDD a yemen ya tabbatar da wannan labarin ya kuma kara da cewa hukumarsa ta tuntubi jami’an gwamnati a San’a don ganin an sake dukkan ma’aikatansu da ake tsare da su yemenawa ko yan kasashen waje. Sannan jami’an tsaro su kawo karshen farwa cibiyoyin hukumar da ke birnin san’a.

Labarin ya kara da cewa jami’an MDD da aka kama sun hada da na ‘World Food Programme, UNICEF da kuma naofishin mai kula da ayyukan MDD a kasar da ya shafi aikin jin kai da kuma bada agaji.

Gwamnatin san’a dai ta bayyana cewa tana zakulo masu aikin leken asirine a cikin ma’aikatan wadan nan hukumomi na MDD. Labarin ya kara da cewa a halinyanzu akway ma’aikatan hukumomin majalisar kimani 50 a tsare. Sannan mafi yawansu yan  kasar ta Yemen ne, wadanda take zarginsuda aikiwa kasashen waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments