Fadar shugaban kasar Venezuela ta yi watsi da maganganun ministan harkokin wajen Amurka Anthony Blinken wanda ya bayyan dan hamayyar siyasar Venezuela Edmund Gonzales a matsayin wanda ya lashe shugaban kasar, tare da bayyana cewa; Abinda Amurkan take yi shi ne kitsa juyin mulki.
Sanarwar fadar shugaban kasar ta Venezuela ta kuma ce; Maganganun da ake dangantawa Blinken suna da hatsari, kuma hakan yana nufin cewa Amruka ta bude fada gaba da gaba da kasar Venezuela.
Venezuela din ta yi tir da abinda Amurkan take yi,tare da kirkirar karairayi da ba su da ma’ana.
A gefe daya, Iran ta bayyana nata cikakken goyon bayan ga gwamnatin Venezuela tare da yin watsi da duk wani kokari na tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan kasar.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Mun yi imani da cewa kasashen Iran da Venezuela suna da karfind a za su iya tafiyar da al’amurransu ba tare da an tsoma musu baki ba.
A jiya ne dai shugaban kasar ta Venezuela ya yi bayani akan yadda tsoma bakin wajen a harkokin cikin gidan kasar yake kokarin haddasa rikici da tashe-tashen hankula, musamman ma dai Amurka.