Gwamnatin Venezuela Ta Yi Tir Da Hare-Haren Amurka A Kan Kasar A Safiyar Yau Asabar

Gwamnatin kasar Venezuela ta zargi kasar Amurka da kai hare hare kan fararen hula da kuma barikin sojoji a birnin Caracas babban birnin kasar ta

Gwamnatin kasar Venezuela ta zargi kasar Amurka da kai hare hare kan fararen hula da kuma barikin sojoji a birnin Caracas babban birnin kasar ta kuma wasu Jihohi.

Tashar talabijan ta Almadaen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar gwamnatin kasar Venezuela tana cewa hare-haren Amurka sun sami wurare a birnin Caracas babban birnin kasar da kuma lardunan Miranda, Aragua da kuma La Guaira.

Caracas ta zargi Amurka da kokarin kwace dimbin arzikin kasar na man fetur da ma’adinai amma tace wannan kokarin ba zai sami nasara ba. Sannan shugaban kasar ta Venezuela bayan hare-haren na Amurka ya shelanta halin ko ta kwana a duk fadin kasar.

Tashar talabijan ta Al-Jazeera na kasar Qatar ta sami wasu hotuna wadanda suka nuna lokacinda makaman Amurka suke fadawa kan barikin sojoji mafi girma a birnin Carakasa ta kuma lokacinda jiragen yakin Amurka suke shawagi kasa kasa a cikin birnin a safiyar yau Asabar.  Sannan dan rahoton Almayadeen ya Caracas yace yaji karar tashin boma-bomai a wasu yankunan masu muhimmanci a birnin Caracas. Sannan Reuters ya ce wutan lantarki ta dauke a wasu yankunan a birnin kusa da tashar jiragen yaki a birnin.

Sai dai labaran da suke fitowa da dumi dominsu daga Amurka sun bayyana cewa Trump ya ce sojojinsa sun kama shugaba Madoro da matarsa sun kuma tafi da su Amurka. Amma wata majiya ta a kasar ta musanta hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted