Gwamnatin Trump na tunanin hana ‘yan kasashe kusan 40 ciki har da Iran shiga Amurka

Gwamnatin Trump na duba yiwuwar sanya takunkumin hana zirga-zirga ga ‘yan kasashen duniya 41 a wani bangare na yaki da kwararar bakin haure da aka

Gwamnatin Trump na duba yiwuwar sanya takunkumin hana zirga-zirga ga ‘yan kasashen duniya 41 a wani bangare na yaki da kwararar bakin haure da aka kaddamar a farkon wa’adin shugaban na Amurka na biyu.

Wani bayanin cikin gida da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nakalto ya nuna cewa an rarraba wadannan kasashe zuwa rukuni uku. Rukunin farko na kasashe goma, da suka hada da Afghanistan, Iran, Syria, Cuba da Koriya ta Arewa, za a sanya musu takunkumi baki daya.

A rukuni na biyu, Eritrea, Haiti, Laos, Myanmar, da Sudan ta Kudu za su fuskanci dakatarwar wani bangare da ya shafi bizar masu yawon bude ido da dalibai, da kuma biza na bakin haure, tare da wasu kebantattu.

Rukuni na uku ya hada da kasashe 26 da suka hada da Pakistan, Belarus da Turkmenistan.

Takardar ta bayyana cewa, wadannan kasashe za su fuskanci wani bangare na dakatar da bayar da bizar Amurka idan gwamnatocinsu “ba su dauki matakan da suka dace don magance matsalar ba cikin kwanaki 60.”

A farkon watan Janairu, Trump ya ba da umarnin zartarwa wanda ke bukatar karin binciken tsaro ga duk wani dan kasar waje da ke son shiga Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments