Gwamnatin Sudan Ba Ta Halarci Zaman Taron Geneva Ba Kan Tattaunawar Rikicin Kasarta

An fara tattaunawar birnin Geneva na kasar Switzerland kan Sudan ba tare da halartar gwamnatin kasar ba Amurka ta yi kira ga sojojin Sudan da

An fara tattaunawar birnin Geneva na kasar Switzerland kan Sudan ba tare da halartar gwamnatin kasar ba

Amurka ta yi kira ga sojojin Sudan da su shiga tattaunawa da nufin tsagaita bude wuta da aka fara a birnin Geneva na kasar Switzerland, tare da halartar dakarun kai daukin gaggawa na kasar.

Tattaunawar dai an shirya za ta dauki tsawon kwanaki 10 karkashin jagorancin Amurka da Saudiyya, da kuma halartar kungiyar Tarayyar Afirka, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Majalisar Dinkin Duniya a matsayin masu sa ido.

Yayin da aka fara shawarwarin, sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya kira shugaban majalisar rikon kwaryar Sudan kuma kwamandan sojojin kasar Abdel Fattah al-Burhan ta wayar tarho, inda ya bukace shi da ya shiga tattaunawar, amma gwamnatin Sudan ta gindaya sharuddar shiga ciki, musamman neman janyewar Dakarun kai daukin gaggawa daga gidajen al’umma da suka mamaye da janyewa daga cikin cibiyoyin gwamnati da kuma rashin amincewar gwamnatin Sudan da halartar wasu bangarorin da Sudan ta dauke su a matsayin masu ruruta wutar yakin kasarta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments