Gwamnatin Saudia Ta Bayyana Bukatarta Na Fadada Harkokin Kasuwanci Da Iran

Mataimakin jakadan kasar Iran a Sudiya ya bayyana cewa kasar Saudia tana bukatar fadada harkokin kasuwanci da kasar Iran. Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya nakalto

Mataimakin jakadan kasar Iran a Sudiya ya bayyana cewa kasar Saudia tana bukatar fadada harkokin kasuwanci da kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya nakalto Mahdi Sufri mataimakin jakadan kasar Iran a saudiya a bangaren tattalin arziki yana fadar haka a hirar da ta hada shi da IRIB-NEWS, a gefen kasuwar baje kolin na ‘ayyukan gwamnati na 13’ a nan birnin Tehran, ya kuma kara da cewa, ya gayyaci ministan harkokin zuba jari na kasar Saudia zuwa ganewa idonunsa irin ci gaban da kasar Iran ta samu a fasahar zamani.

Sufri ya kuma kara da cewa nan da watanni biyu ko uku masu zuwa ne kwamitin tattalin arziki na kasashen biyu zai bude zama, don tattauna al-amuran tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Hari la yau kwamitin zai tattauna al-amura daban daban da suka shafi fadada ayyukan tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Sufri ya kamala da cewa, daya daga cikin al-amuran da ofishinsa ya sa a gaba shi ne batun ‘Transit” saboda a shekara ta 1402 da ta gabata ‘Transit ya ta Iran ya kai ton miliyon 17, wanda ya samar da kudade kimani dalar Amurka biliyon 7.1 sannan ana saran a wannan shekara ta 1403 zai kai ton miliyon 20.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments