Gwamnatin Nijar, ta saki ministocin hambarariyar gwamnatin Bazoum

Gwamnatin Nijar ta saki kusan mutane 50 da suka hada da ministocin da aka tsare tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum

Gwamnatin Nijar ta saki kusan mutane 50 da suka hada da ministocin da aka tsare tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.

Baya ga tsaffin ministocin da akwai wasu sojoji da ake zarginsu da yunkurin juyin mulki a shekarar 2010 da suma aka sake su.

 “An sako wadannan mutane ne bisa ga shawarwarin da babban taro na kasar ya bayar,” kamar yadda sakataren gwamnatin kasar ya karanta a gidan talabijin din kasar a cikin daren jiya.

Cikin tsaffin ministocin da aka saki har da tsohon ministan man fetur Mahamane Sani Issoufou, dan tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou, da kuma tsohon ministan tsaro Kalla Moutari, da tsohon ministan kudi Ahmat Jidoud, da kuma tsohon ministan makamashi Ibrahim Yacoubou.

An kuma saki sojojin da a baya aka samu da laifin yunkurin juyin mulki da kuma janyo “barazana ga tsaron kasar”, ciki har da Janar Salou Souleymane, da tsohon babban hafsan hafsoshin sojin kasar, da wasu jami’ai uku da aka yankewa hukuncin daurin shekaru 15 a shekarar 2018 a gidan yari, saboda kokarin hambarar da Shugaba Issoufou a shekarar 2015.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments