Tun shekara ta 2018 ne gwamnatin kasar Kamaru ta bude cibiyoyi guda biyu, don horaswa da kuma dai-daita fahintar addini na ‘ya’yan kungiyar Boko Haram kimani 3000 da suka kama.
Har’ila yau da koya masu sana’o’i saboda su sake komawarsu a cikin al-umma.
Shafin yanar gizo na ‘Afrika News’ ya nakalto Evariste Atangana, gwamnan lardin Arewacin kasar Kamaru, yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa: A nan Meri muna da tsoffin mayakan boko haram kimani 3000 wadanda muka sake basu horaswa a cikin wannan cibiyar, sannan a yau mun yaye 600 daga cikinsu, don su sake komawa cikin mutane.
Gwamnan ya kara da cewa: zamu ci gaba da sanya ido a kansu, don tabbatar da cewa sun sauya halayensu da rayuwarsu zuwa yanda ya dace, da gaske.