Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza

Gwamnatin mamayar Isra’ila ta yanke hukuncin kisa kan masu fama da cutar kansa da kuma waɗanda suke fama da matsalar koda na mutuwa a Gaza

Gwamnatin mamayar Isra’ila ta yanke hukuncin kisa kan masu fama da cutar kansa da kuma waɗanda suke fama da matsalar koda na mutuwa a Gaza domin hana fitar da su wata kasa don neman magani

Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Gaza ta bayyana matukar damuwarta game da tabarbarewar lafiyar marasa lafiya da ke fama da cutar kansa da kuma cutar koda a Zirin Gaza. Wadannan cututtuka sun kara ta’azzara ne sakamakon hare-haren sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza da kuma ci gaba da killace yankin bayan tsagaita bude wuta, gami da hana shigar dq magunguna da kayayyakin ayyukan likitanci masu muhimmanci cikin yankin. Cibiyar ta kuma yi nuni da tsauraran matakan fitar da marasa lafiya zuwa ƙasashen waje don neman magani.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, Cibiyar ta tabbatar da cewa, wannan yanayin ba shi da wata shakka cewa Isra’ila na aiwatar da manufar kisan gilla a kan dubban marasa lafiya ta hanyar hana su ‘yancinsu na rayuwa da magani da gangan, da kuma canza wahalarsu zuwa wani nau’in hukunci na gama gari.

Cibiyar ta ambaci majiyoyin lafiya da ke tabbatar da cewa, akwai marasa lafiya 12,500 da ke fama da cutar kansa a Zirin Gaza, ciki har da ƙananan yara. Ta lura cewa mata sun kai kusan kashi 52% na dukkan masu cutar kansa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments