Kungiyar kare hakkin fursunoni a Falasdinu da aka mamaye, wacce ake kira ‘Samidoon’ ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI ta bada umurnin tsare falasdinawa 91 ba tare da gabatar da su a gaban kotu don sanin alifin da suka aikata ba.
Jaridar ‘The Combo’ ta wannan kungiyar ta Sanya hotunan mutane biyu daga cikin falasdinawa 91 wadanda sojojin yahudawan suka kama a ranakun 30 ga watan Nuwamba da kuma jiya daya da watan Dicemba na wannan shekarar.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin yahudawan ta kafa wata doka wacce zata basu damar tsare Falasdinawa kawai, na tsawon lokacinda suka ga dama.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa daga cikin falasdinawan da sojojin HKI ta kama ta kuma tsare da sunan wannan dokar sun hada, da lawyoyi, yan jaridu, yan jami’a da sauransu.
Kuma a ranakun Asabar da lahadin da suka gabata ne sojojin yahudawan suka yi masu kofar rago suka kamasu suka tafi da su suka kama tsaresu.
Asem Mustafa da Isma’il Ibrahim Khalil Khabas, daga garin Jenin na yankin yamma da kogin Jordan, na daga cikin wadanda yahudawan suka tsare.
Ya zuwa yanzu dai falasdinawa daga yankin yamma da kogin Jordan kimani 3,443 ne suke tsare karkashin wannan dokar. Sannan jimillan Falasdinu 10,200 ne gwamnatin HKI take tsare da su daga yankin.