Gwamnatin Biritaniya ta yi furuci da karfin sojin Yemen da na dakarun sa-kan kasar na kungiyar Ansarullahi ta mabiya Huthi
Gwamnatin kasar Birtaniya ta yi furuci da cewa; Makaman kasar Yemen masu inganci ne kwarai lamarin da sanya suka bullo da wani sabon salo na soji domin fuskantar makiyansu a tekun Bahar Maliya, sakamakon haka Birtaniya ta jaddada aniyarta na daukan sabbin matakan yaki da inganta makamanta domin samun damar tunkarar sojojin na Yemen.
Sakataren tsaron kasar Birtaniya Grant Shapps a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa: Ganin yadda ‘yan Yemen suke amfani da jiragen sama marasa matuka ciki a ayyukan sojinsu na ruwa, to, a bayyane yake cewa Birtaniyya tana bukatar yin aiki da wani sabon salon karfin soji na zamani, kuma dole ne ta sabunta karfin tsaronta.
Ya kara da cewa: A cikin kasa da shekara guda, sun tilastawa sojojin ruwa yin amfani da makamai mai linzami sau da dama, lamarin da bai faru ba a shekarun baya. Yana mai nuni da cewa gwamnati ta bullo da wani shiri na kara kashe kudaden tsaro zuwa kashi 2.5%.