Gwamnatin Amurka ta gargadi haramtacciyar kasar Isra’ila kan kaddamar da hare-hare kan kasar Lebanon
Jami’an gwamnatin Amurka sun gargadi ministan tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, Yo’av Gallant, game da duk wani yunkurin mamaye wani yanki na kudancin Lebanon, saboda hakan zai haifar da barkewar yakin basasa a yankin.
Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Ha’aretz” ta watsa rahoton cewa: Jami’an Amurka sun shaidawa Gallant, a ziyarar da ya kai birnin Washington na Amurka a wannan mako cewa: Duk wani yunkurin da haramtacciyar kasar Isra’ila zata yi na kaddamar da iyakantaccen hari a kudancin Lebanon, hakan zai kai ga barkewar yakin basasa da kungiyar Hizbullah, a bisa ga rahoton sirri na Amurka da aka gabatar wa jami’an gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.
Wani jami’in Amurka a tattaunawar da ya yi da jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana cewa: Ko da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi da’awar cewa manufarta na kaddamar da hari kan yankin kasar Lebanon ita ce nisanta mayakan kungiyar Hizbullah daga kan iyakar Isra’ila, kuma ba ta dauke da aniyar ruguza birnin Beirut, to, dayan bangaren ba zai amince da hakan ba, don haka akwai yiwuwar barkewar yakin ya haifar barna mai girma ga dukkanin bangarorin biyu.