Gwamnati da kuma jami’an yan sanda a kasar Amurka suna dirar mikiya a kan daliban jami’o’ii da kuma malamansu Masu Goyon Bayan Falasdinawa

Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu a yau zai yi Magana ne danganeda yadda gwamnati da kuma jami’an yan sanda a kasar Amurka suke

Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu a yau zai yi Magana ne danganeda yadda gwamnati da kuma jami’an yan sanda a kasar Amurka suke dirar mikiya a kan daliban jami’o’ii da kuma malamansu wadanda suke fitowa a kan tiyuna a cikin jami’o’insu suke kuma bayyana rashin amincewarsu da ci gaba da kissan kare dangi wanda sojojin HKI tare da makaman gwamnatin Amurka suke ci gaba da yi a zirin gaza, ko kuma kasar falasdinu da aka mamaye. Ni Tahir amin ne zai karanta maku sharhin kamar haka.

///…A yaynda daliban Jami’o’ii a kasar Amurka, suke ci gaba da fitowa zanga-zamgar nuna rashin amincewarsu da ci gaba da kisan kare dangi wanda sojojin JKI suke yi a Zirin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye, a dayan bangaren kuma jami’an tsaro a kasar sun ci gaba da dirar mikiya a kan masu zanga –zangar wadanda suka hada Dalibai, malamai da kuma ma’aikatan jami’o’in.

Donal Arl Clinize, wani malami a Jami’ar Washington ya bayyana a cikin wani rubutun da yayi, dangane da yadda gwamnati da kuma Jami’an yansanda a Amurka suke dirar mikiya kan daliban Jami’o’ii daban daban a kasar, wadanda suke goyon bayan Falasdinwa, suke kuma son a kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza, wanda kuma tare da taimakon gwamnatin Amurka take yi, ya bayyana cewa  wannan halin har yanzun yana ci gaba, kuma jami’an tsaro suna kara karfi wajen murkushe masu zanga-zangar suna kuma kara kuntata masu.

Y ace wannan halin yana ci gaba, ‘yansanda suna ci da kama dalibai da malamansu su rufe a gidajen yari. A wani bangare kuma Jami’o’ii da dama sun hana dalibai wadanda suka shiga cikin masu goyon bayan Falasdinawa takardunsu na kammala Jami’a. Wasu daliban kuma an koresu daga jami’o’iin, a yayinsa wasu kuma an yi masu barazanar baza’a basu takardun shaidar kammala jami’o’insu.

Yau foye da shekara guda, ko kuma kimani watanni 14 kenan, sojojin HKI suke ci gaba da kissan kare dangi, tare da hana abinci da magunguna da ruwa shiga zirin na Gaza.

Tun shekara ta 2023 ne daliban Jami’o’ii a kasashen Amurka da Turai suke fitowa zanga-zangar yin All..wadai da kissan kiyashin da HKI tare da taimakon kasashen yamma da kawayensu, suke fitowa kan tituna a wadannan kasashe suke kuma nuna rashin amincewarsu da hakan. Da kuma gabatar da bukata na a dakatar da wannan yakin na fin karfi.

A dai-dai lokacinda wannan yakin yake ci gaba, a dai-dai lokacinda ake ci gaba da zubar da jinin Falasdinawa, masu adawa da shi ma, sun ci gaba da zanga-zanga, a yayinda Jami’an tsaro a wadannan kasashe suka kara yawan jami’an tsarosu, wadanda suke murkushe masu zanga-zanga a wadannan kasashen musamman kasar Amurka.

Duk tare da shi’arin encin fadin albarkacin baki wanda yan siyasar wadanda kasashe suka yadawa, amma a wannan karon sun manta da shi, saboda yadda suke dirar mikiya don rufe bakin wadannan daliban Jami’o’ii da kuma malamansu wadanda suke fadin al-barkashin bakinsu, na a kawo karshen yaki a Gaza a kuma dakatar da zubar da jinin Falasdinawa, har’ila yau sun ci gaba da bukatar sojojin yahudawan Isra’ila sun kawo karshen mamayar da sukewa kasar Falasdinu shekaru kimani 80 da suka gabata.

Wadannan shi’arai na kare hakkin bil’adama da kuma hakkin fadin albarkacin baki, ba abin mutuntawa ne a wajen wadannan kasashe, idan abi ya shafi Falasdinawa ko kuma kasashen larabwa da musulmi a wannan zamanin.

Kare hakkin bil’adama a wadannan kasashe, da kuma fadin albarkacin baki, sai in abinda ya shafi kasashen yamma ko wadanda suke tare da su musamman HKI. Kissan kare dangi wanda yahudawan sahyoniya,suke yi a gaza fiye da watanni 14 da suka gabata, kare kanta ne, inda shuwagabannin kasashen yamma. Hakkinsu ne su kare kansu daga Falasdinawa, ta hanyar hanasu abinci da magunguna da rusa gine-gine a Gaza da sauransu.

Amma duk tare da dirar mikiya, da matsin lamban da gwamnatocin kasashen yamma sukewa daliban Jami’o’ii da kuma malamansu, bai hanasu ci gaba da fitowa suna allawadai da HKI da kuma gwamnatocin kasashensu wadanda suke taimaka mata a cikin ta’asan da take aikatawa a Gaza ba. Suna kuma ci gaba da bayyana bukatarsu ta kawo karshen yaki a Gaza da kuma kawo karshen mamayar da HKI takewa kasashen larabawa a yankin Asiya ta kudu ba.

Jaridar yahudawan Sahyoniya, mai suna {Yadi’ud Aharunut ya bada labarin cewa a cikin halin da ake ciki wasu Jami’I’oii a kasashen Amurka da Canada, sun kulla yarjeniyoyin tsaro da kamfanonin tsaro na HKI da dama, don murkushe zanga-zangar da daliban jami’o’ii, masu goyon bayan Falasdinawa,  a wadannan kasashe suke jagoranta.  
Jaridar ta kara da cewa, tare da zaben Donal  Trump a matsayin shugaban kasar Amutrak, ya yi alkawarin zai ci taran duk wata jami’a ko wata cibiyar ilmi a kasar Amurka wacce bata maganin dalibai da malamanta wadanda suke goyon bayan Falasdinawa ba.

Wannan ba shi ne karon farko wanda gwamnatin kasar Amurka da kawayenta suke daukan irin wadannan matakan kan al-amura wadanda basu yi dai-dai da bukatunsa. Suna nuna fuska biyu a duk abinda ya shafi maslharsu, a nan su ne suna kare hakin bil’adama da fadin albarkacin balki, idan kuma abu guda ya auku a wani bangaren da basa so sais u sabawa matsayinsu na farko.

Josept Mosad wani malamin Jami’ar Colombia da ke birnin NewYok ya bayyana a cikin wani rubutun da yayi, kan cewa:

Jami’o’ii a kasar Amurka da kuma masu ra’ayin Libral Democrats, wato masu yencin fadin albarkacin baki, zasu kiyaye wadannan ka’idoji ne kawai idan sun zo kan masalaharsu, kan abinda suke so. Amma idan hakan ya shafi makiyinsu ne to ba zasu taba yi masa adalci ba.

Sannan: Ya kara da cewa, al-amarin kasar Falasdinu da kuma yadda HKI take kissan kiyashin ga falasdinawa a gaza, wani al-amari ne wanda yake farkar da dalibai da malaman Jami’o’ii a kasar yamma, kuma duk abinda gwamnatocin wadanda kasashe zasu yi ba zasu iya dushe shi ba. Don haka duk tare da murkucesu da za’a yi ko a cutar da su, wannan ba zai hana wannan wayewar kan ci gaba ba, don dabi’ar mutum wanda yake da lafiyeyyen kwakwalwa ya ki amioncewa da wannan zaluncin da rashin adalcin a ko ina yake a duniya.

==========================.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments