Guterres Ya Yi Tsokaci Dangane Da Martanin Kungiyar Hamas Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Gaza

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya yayi tsokaci kan martanin kungiyar Hamas kan yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya yayi tsokaci kan martanin kungiyar Hamas kan yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana jin dadinsa da martanin da kungiyar Hamas ta mayar dangane  shirin shugaban Amurka Donald Trump kan Gaza, yana mai bayyana hakan a matsayin abin karfafa gwiwa.

Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a cikin wata sanarwa a yau Asabar cewa: Guterres ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su yi amfani da wannan damar wajen kawo karshen yakin Gaza da kuma kawo karshen bala’in jin kai da fararen hula ke fuskanta.

Ya kara da cewa, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya tabbatar da shirin Majalisar Dinkin Duniya na goyon bayan duk wani yunkurin kasa da kasa da ke da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take da kuma samar da yanayin samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted