Guterres Ya Bukaci A tsagaita bude wuta cikin gaggawa a zirin Gaza

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a zirin Gaza, da kuma sakin mutanen da

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a zirin Gaza, da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma kara kai agaji ga yankin Falasdinawa da aka yi wa kawanya.

“Ina sake nanata kira na, kiran da daukacin duniya ke yi na a tsagaita bude wuta na jin kai cikin gaggawa, da a sako duk wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba da kuma a kara kai agajin gaggawa.

Zai jima ba’a murmure ba daga barnar da wannan yaki ya yi mana,” in ji shi a wani jawabi ta bidiyo a taron masu ba da agaji na kasa da kasa a Kuwait.

Kiran na Guteress, na zuwa ne kwana guda bayan da Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar da ya tabbatar da ‘yancin Falasdinawa ta hanyar amincewa da kasar a matsayin mamba a majalisar.

Kudirin da UAE ta gabatar ya samu amincewar kasashe 143, yayin da 25 suka ce ba ruwan su, sai guda 9 da suka ki amincewa, da suka kada kuri’ar kin amincewa da suka hada da : Amurka, Isra’ila, Argentina, Jamhuriyar Czech da Hungary.

Daftarin ya fayyace cewa Falasdinu ta cika sharuddan da ake bukata don zama memba,” kuma “don haka ya kamata a shigar da ita cikin Kungiyar.”

Masana na ganin wannan babban sako ne da aka aika wa kwamitin sulhu da Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments