A lokacin wani taro da ya gudana tsakanin shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan da kuma babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio gutteres a kasar china ya bayyana cewa iran tana da hakkin ta mallaki fasahar nukiliya na zaman lafiya, kana ya nuna damawarsa game da batun takunkumi da kasashen turai ke son sake kakabawa iran,
Wannan bayanin na Gutteres ya kara fito da matsayin iran a mataki na kasa da kasa na hakkin mallakar fasahar nukiliya domin ayyukan zaman lafiya, a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun tankiya tsakanin iran da kuma kasashin turai game da shirin ta na nukiliya da kuma yunkurin sanya mata takunkumai,
A nasa bangaren shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya bayyana cewa hukumar kula da makamamin nukiliya ta duniya IAEA ba ta yi ko da Allah wadai da harin da HKI ta kai kan cibiyoyin nukiliya iran na zaman lafiya ba, da take gudanar da ayyukanta karkashin kulawarta, iran tana daya daga cikin wadanda suka fuskanci hare –haren ta’addanci tun daga lokacin da aka kafata, saboda da yawa daga cikin masananmu da manyan jami’anmu sun yi shahada sakamakon hare-haren ta’addanci da aka kai musu.