Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres ya bayyana matukar damuwa game da halin da ake ciki a Gaza, yana mai cewa “babu wani tudun-mun-tsira” a baki dayan Zirin.
” bala’in da ke faruwa a Gaza ya wuce a misalta shi,..Kowane sashe na yankin yana iya zama wurin kisa,” in ji Guterres a sakon da ya wallafa a shafin X.
Ya kara da cewa lokaci ya yi da bangarorin su jajircewa wajen yarjejeniyar tsagaita wuta.
A gefe guda, Stephane Dujarric, wanda shi ne mai magana da yawun Guterres ya ce MDD tana kira ga dukkan bangarorin su yi biyayya ga dokokin jinkai na duniya sannan su yi matukar taka-tsantsan don “tsare rayukan fararen-hula da dukiyoyinsu.”
“Ina mai shaida muku cewa mu da abokan aikinmu na bayar da agajin jinkai za mu ci gaba da taimaka wa iyalan da aka tilasta wa barin arewacin Gaza zuwa kudanci,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai.
Akalla karin Falasdinawa 49 ne aka kashe a harin da Isra’ila ta kai a Gaza, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu zuwa 38,713 tun daga ranar 7 ga Oktoban da ya gabata, in ji ma’aikatar lafiya a yankin da aka yi wa kawanya.
“Sojojin Isra’ila sun kashe mutane 49 tare da raunata wasu 69 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata,” in ji ma’aikatar.