Guteress Ya Yi Gargadi Game Da Barkewar Rikici Tsakanin Isra’ila Da Lebanon

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadi game da barkewar rikici a yammacin Asiya bayan da Isra’ila ta yi barazanar kaddamar da

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadi game da barkewar rikici a yammacin Asiya bayan da Isra’ila ta yi barazanar kaddamar da farmaki a Lebanon.

Da yake zantawa da manema labarai a birnin New York, babban jami’in na MDD ya ce hadarin da ke tattare da rikici a yankin na kara fadada, yana mai nuni da yadda ake ci gaba da yin musayar wuta a kullum da musayar zafafen kalamai tsakanin gwamnatin Isra’ila da kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya.

“Tilas a yau in bayyana matukar damuwata game da ci gaba da tabarbarewar da ake samu tsakanin Isra’ila da Hizbullah a yankin Blue Line.

Babban jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya ce al’ummar yankin da duniya baki daya ba za su bari ” Lebanon ta zama wata Gaza ba.”

Dole ne a kare fararen hula, bai kamata a kai hari ga yara ba, ‘yan jarida da ma’aikatan kiwon lafiya ba, kuma al’ummomin da suka rasa matsugunansu dole ne su koma gidajensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments