Shugaban ofishin jagoran juyin musulunci na Iran, Hujjatul Islam Wal Muslimina Muhammad Gulpayagani ya bayyana yunkurin nan na: Goyon Bayan Iran.” Da cewa, aikin da suke yi yana a karkashin amsa kiran jagoran juyi ne wanda ya yi kira da a taimakawa waddanda su ka cutu daga hare-haren HKI.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto Hujjatul-Islam Muhammad Gulpayagani yana bayyana muhimmin matakin da Ayatullah Khamnei yake dauka a fagen gwgawarmaya, yana mai kara da cewa; Shi ne wanda yake dauke da tutar gwgawarmaya akan wannan tafarkin cikin dogara da Allah madaukakin sarki da tafiya akan tafarkin Ahlul Bayti ( a.s).
Hujjatul-Islam golpayagani ya ambaci wasu ayyukan da yukurin na Iran take yi wajen taimakawa wadanda su ka cutu daga hare-haren ‘yan sahayoniya , inda ya bayyana yadda mata su ka bayar da zobbonsu na aure, wasu mutanen kuma su ka sadaukar da gidajensu.
Muhammad Golpayani ya kuma kara da cewa; Aikin da jagoran juyin musuluncin yake yi ci gaba ne da aikin da malaman musulunci na baya su ka yi akan tafarkin raya addinin musulunci.