Ghazizadeh : Zamu Dora Bisa Tafarkin Ra’isi Na Karfafa Huldar Diflomatsiyya  

Dan takara a zaben shugaban kasa Iran, Amir Hossein Ghazizadeh Hashemi ya ce zasu dora kan tafarkin mirigayi shugaban kasar na karfafa diflomatsiyya da kasashen

Dan takara a zaben shugaban kasa Iran, Amir Hossein Ghazizadeh Hashemi ya ce zasu dora kan tafarkin mirigayi shugaban kasar na karfafa diflomatsiyya da kasashen duniya, idan aka zabe shi kan karagar mulki a zaben shugaban kasar da aka ranar 28 ga watan Yuni.

A muhawarar da aka shirya gidan talabijin, Ghazizadeh Hashemi, ya ce siyasar mirigayin ta haifar da da mai ido sosai a kasar.

Dan takaran ya bada misali da “Siyasar man fetur din kasar wacce a baya tana tsakanin ganga dubu 100 zuwa 600, ya haura ganga miliyan daya da rabi,” in ji shi, yana mai bayyana yadda Iran ta shiga cikin sassan duniya kamar kungiyar hadin gwiwar Shanghai (SCO) da BRICS a matsayin gagarumin ci gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments