Gaza : Spain na son gurfanar da Isra’ila gaban ICC kan cin zarafin masu fafutukar kai agaji

Gwamnatin Spain, ta fara wani yunkuri na ganin an gurfanar da Isra’ila a gaban kotun hukuntan manyan laifuka ta Duniya wato ICC, kan cin zarafin

Gwamnatin Spain, ta fara wani yunkuri na ganin an gurfanar da Isra’ila a gaban kotun hukuntan manyan laifuka ta Duniya wato ICC, kan cin zarafin ayarin masu fafatukar neman shigar da agajin jin kai zuwa Zirin Gaza.

Biyo bayan shaidar da ‘yan kasar Spain suka bayar na zargin cin zarafin da sojojin Isra’ila suka yi musu a lokacin da suke tsare da su bayan kutsawar jirgin ruwa na Global Sumud, Spain ta sanar da cewa za a iya daukar matakin shari’a a gaban kotun ta (ICC).

A wata hira da gidan talabijin na TVE, ministan harkokin cikin gida na Spain Fernando Grande-Marlaska ya bayyana damuwarsa game da cin zarafin.”

Ya bayyana farmakin na Isra’ila kan jiragen ruwa a cikin ruwa na kasa da kasa a matsayin “tauye ‘yancin kai ga wadanda abin ya shafa.”

Ya sake tabbatar da cewa za a binciki laifukan wadanda watakila aka azabtar da su ta hanyoyin da suka dace na kasa da na kasa.

Marlaska ya kuma tabbatar da cewa ofishin babban lauyan su ya bude bincike.

Wadannan kalamai na zuwa ne bayan da aka kori masu fafutuka a zirin Gaza daga yankunan da Isra’ila ta mamaye.

Sojojin Isra’ila sun kai samame tare da kwace jiragen ruwa na Sumud Global Flotilla, inda suka kame sama da masu fafutuka 450 daga kasashe sama da 40.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments