Search
Close this search box.

Gaza: Sojojin HKI Sun Kai Hare Hare Kan Wata Makarantar MDD Inda Ta Kai Falasdinawa Da Dama Ga Shahada

Jiragen yakin HKI sun kai hare hare kan wata makarantar MDD wato UNRWA da ke garin Nusairat a tsakiyar Zirin gaza, inda Faladinawa da dama

Jiragen yakin HKI sun kai hare hare kan wata makarantar MDD wato UNRWA da ke garin Nusairat a tsakiyar Zirin gaza, inda Faladinawa da dama suka rasa rayukansu wasu kuma suka ji rauni

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa,  ba wannan ne karon farko wanda  jiragen yakin HKI suke kai hare hare kan makarantun UNRWA ba.

Sai dai kamar yadda suka saba, sojojin HKI sun bada sanarwan kai hare hare kan makarantar ta UNRWA da ke Nusairat, amma sun kara da cewa Hamas ta maida makarantar cibiyar sojojinta. Don haka ne suka  halatta jinin duk wanda yake cikin makarantar.

A wani labarin kuma sojojin HKI sun ci gaba da kai hare hare da makaman atilary kan wurare daban daban a yankin na Gaza. Hare hare wadanda suka lakume rayukan falasdinawa da dama mafi yawan mata da yara kanana.

Philippe Lazarina kwamishina mai kula da Hukumar UNRWA ta MDD ya bayyana cewa tun fara yakin Tufanul Aksa zuwa yanzo sojojin HKI sun kai hare hare kan cibiyoyun hukumar har guda 190 a gaza. Hare haren da suka kai Falasdinawa kimani 520 ga shahada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments