Search
Close this search box.

Gaza: Jiragen Yakin Isra’ila Sun Kaddamar Da Munanan Hare-Hare A Gabashin Rafah

Kafafen yada labaran yahudawan Sahyuniya sun ce da sanyin safiyar yau Talata sojojin Isra’ila sun fara kaddamar da wani farmaki a gabashin Rafah da ke

Kafafen yada labaran yahudawan Sahyuniya sun ce da sanyin safiyar yau Talata sojojin Isra’ila sun fara kaddamar da wani farmaki a gabashin Rafah da ke kudu da zirin Gaza da manyan  makamai.

Kafofin yada labaran sun bayar da rahoton cewa, jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-haren ne ta sama a gabashin Rafah.

Sojojin Isra’ila sun tabbatar a yammacin ranar Litinin cewa, za su ci gaba da gudanar da ayyukan yaki a zirin Gaza, a daidai lokacin da suke nazarin martanin da Hamas ta mayar kan shirin sulhu da musayar fursunoni da kungiyar ta amince da shi.

Ofishin firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kuma sanar da cewa, gwamnatin Isra’ila baki daya ta amince da ci gaba da kai farmaki a birnin Rafah, domin kara matsin lamba a kan Hamas.

A daya bangaren kuma, ofishin Netanyahu ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, Tel Aviv za ta aike da tawaga don ganawa da masu shiga tsakani don kokarin cimma yarjejeniya mai karbuwa.

Tankokin yakin Isra’ila sun shiga birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza, inda suka kutsa kai kusan mita 200 a gabashin garin, kamar yadda wani jami’in tsaron Falasdinu da wani jami’in Masar suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments