Jiragen yakin HKI, a wasu sabbin hare haren da suka kai kan yankin Gaza a jiya Lahadi, sun jefa boma bomai kan makarantun ‘Annasr’ da kuma ‘Hassan Salama’ a yammcin zirin Gaza, inda suka kai falasdinawa da dama ga shahada, a yayinda wasu da dama suka ji rauni.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa bayan da gwamnatin Natanyahu ta kasa cimma manufofinta a Gaza bayan fara yakin Tufanul Aksa watanni kimani 10 da suka gabata, a halin yanzu ta koma kan daukar fansa a kan farare hula wadanda suke samun mafaka a makarantun yankin.
Labarin ya kara da cewa a jiya da yamma ne jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan mata da yara da tsoffi wadanda suke samun mafaka a makarantun ‘Hassan Salama’ da kuma ‘Annasr’ na yammacin Gaza, inda suka kashe akalla falasdinawa 30 a lokaci guda. Sannan wasu da dama suka ji rauni. Akwai yiyuwar yawan wadanda suka yi shahada ya karu saboda munanan raunukan da wasu suka samu a hare haren.
Mahmood Basil kakakin kungiyar kare fararen hula a Gaza ya bayyana cewa ana cikin wani mummunan hali a Gaza, ya kuma kara da cewa, kashi 80% na wadanda suka yi shahada a hare haren makarantun ‘Annasr da kuma ‘Hassan Salama’ yara ne wadanda suke samun mafaka a makarantun bayan an rusa gidajensu a gaza.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta gaza ta bada sanarwan cewa daga fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata, ya zuwa yanzu Falasdinawa 39,583 ne suka tabbatar da shahadarsu, a yayinda wasu dubu 91,398 suka ji rauni. Sannan ana ganin wasu falasdinwa fiye da 10,000 suna bisne a karkashin kasa. A yayinda wasu dubban kuma suke tsare a gidajen yarin HK.