A cikin makonni biyu da Isra’ila ta shafe tana kaddamar da kazamin farmaki a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza, Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kashe Falasdinawa fiye da 770, a cewar wata sanarwa da ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar a ranar Laraba.
Sama da Falasdinawa 1,000 ne aka jikkata yayin hare-haren, yayin da wasu fararen hula sama da 200 da suka hada da mata da kananan yara Isra’ila sun yi garkuwa da su.
Ofishin yada labarai na Gaza ya kuma yi gargadin cewa sama da mutane 100,000 da suka jikkata da marasa lafiya a arewacin Gaza na cikin tsananin bukatar agajin gagagwa. Sai dai har yanzu ba a iya samun isar da agajin ba, yayin da hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama ta lalata asibitoci hudu a yankin, a wani bangare na ayyukan kisan kare dangi da ake ci gaba da yi.
A cikin wani faifan bidiyo da hukumar bayar da agaji ta Falasdinu ta fitar, ta ce an yi lugudne wuta kan masu bayar da agajin gaggawa a lokacin da suke kokarin ceto fararen hula bayan wani harin da jirgin sama ya kai kan wani gidan iyali a yankin Fakhoura na Jabalia.
Sansanin ‘yan gudun hijirar ya kasance cibiyar aikin kisan kare dangi na “Isra’ila” na tsawon kwanaki 19, tare da fadada hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a yankunan da ke kusa, ciki har da Beit Lahia da Beit Hanoun.
Yayin da ake ci gaba da yin kisan kiyashi, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa babu wata mota da ke dauke da abinci, ko ruwa da kuma magunguna da ta shiga arewacin Gaza tun daga ranar 30 ga watan Satumba.
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres da shugabannin kasashen duniya da dama sun yi Allah-wadai da yadda Isra’ila ke kashe fararen hula sakamakon wuce gona da iri da take yi.