Gaza : Harin Isra’ila Ya Yi Ajalin Falasdinawa Da Dama A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira Na Nuseirat

Bayanai daga Falasdinu na nuni da cewa adadin Falasdinawan da sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 37,347 galibi

Bayanai daga Falasdinu na nuni da cewa adadin Falasdinawan da sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 37,347 galibi mata da kananan yara, tare da jikkata wasu 85,372.

Adadin ya karu ne sakamakon hare haren da Isra’ila da ke ci gaba da kai a zirin.

Ko a daren ranar Litinin zuwa Talata, jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare ta sama kan sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa akalla 17.

Harin na farko ya yi sanadiyar mutuwar mutane 10 da suka hada da mata da kananan yara tare da jikkata wasu da dama.

Biyar daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ‘yan gida daya ne, kamar yadda tashar Al Jazeera ta ruwaito, ta kuma kara da cewa adadin wadanda abin ya shafa na iya karuwa yayin da wasu mutane suka bace a karkashin baraguzan ginin.

Ko a kwanakin baya ma Isra’ila ta kai wani mummunan hari a sansanin ‘yan gudun hijirar na Nuseirat, inda suka kashe Falasdinawa sama da 270 tare da jikkata wasu kusan 700 na daban, inda sojojin na mamayar sukayi ikirarin kubutar da mutane hudu da aka yi garkuwa da su a yayin wannan kazamin harin.

Kwararru kan kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da kisan kiyashin da suka kira “daya daga cikin munanan ayyuka” na yakin da Isra’ila ke yi da Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments