A wata sanarwa da Haramtacciyar Isra’ilan ta fitar, ta ce, daga nan zuwa sa’o’i 36 masu zuwa za ta dakatar da aikin kungiyoyin agaji masu yawa, bisa riya cewa, ba su mika bayanan ma’aikatansu ba na cikin Gaza da kuma wadanda su ka zo daga waje.
Daga cikin kungiyoyin da akwai “Action Aids” da “Doctors Without Borders” da kuma wasu da dama.
A can cikin nahiyar turai, ma’aikatun harkokin wajen kasashe 10 sun fitar da bayani na nuna damuwarsu akan wannan matakin. Kasahsen kuwa sun hada, Birtaniya, Canada, Denmark, Finland, Faransa da Swedeen. Sai kuma Iceland, Japan, Norway da Swiss land.
Ma’aikatun harkokin wajen wadannan kasashen sun fitar da sanarwa ce ta bai daya akan damuwarsu saboda wannan matakin na “Isra’ila da zai kara jefa Falasdinawan cikin tabarbarewar yanayi.
Kasashen sun bayyana matakin da cewa; wani bababba bala’i ne.”
Haka nan kuma sun ce, farafen hula a cikin Gaza suna cikin mawuyacin hali mai tayar da hankali, ga shi kuma ana karatar lokacin sanyi. Kuma da akwai mutane miliyan 1.3 da suke da bukatuwa da taimako na matsungunni.
Wata mastalar da kasashen 10 su ka lissafo ita ce, ta rashin magunguna da sauran muhimman kayan agaji.
A gefe daya, ministocin 10 sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da masu aiki da ita da su ci gaba da aiki tukuro domin kawo karshen tarnakin da Isra’ila take kawo wa ayyukanta a Gaza.
Wata matsalar da ake fuskanta wacce “Isra’ila” ce ta kirkireta ita ce hana shigar da wasu nau’oi na kayayyaki cikin Gaza, bisa fakewa da cewa za a iya amfani da su ta a fagen aikin soja.
A dalilin haka, kasashen 10 sun bukaci ganin an bude dukkanin hanyoyin shigar da kayan agaji zuwa cikin Gaza da dauke duk wani tarnaki.