Hukumomi a Gaza sun ce akalla Falasdinawa 357 ne sukayi shahada yayin da wasu 903 suka jikkata a hare-haren Isra’ila tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.
Yawancin wadanda abin ya shafa mata ne da yara, in ji ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza a cikin wata sanarwa.
A cewar ofishin, sojojin Isra’ila na kuma tsare da mutane 38 ba bisa ka’ida ba.
ofishin ya ce ya lissafa laifukan tsagaita wuta guda 591, ciki har da harbi kai tsaye kan fararen hula, gidajensu, da tantuna, da kuma bama-bamai da rushe gidaje.
Sanarwar ta ce, wadannan laifukan, suna “nufin mamayar na wargaza yarjejeniyar da kuma haifar da mummunan yanayi wanda ke barazana ga tsaro da kwanciyar hankali a yankin Gaza.”
Ofishin ya yi kira ga Shugaban Amurka Donald Trump, da masu shiga tsakani da kuma masu ba da garantin tsagaita wutar, da kuma Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da su dauki matakai masu inganci don kawo karshen hare-haren Isra’ila da kuma tilasta wa Tel Aviv ta bi dukkan ka’idojin yarjejeniyar.
Yarjejeniyar tsagaita wuta, wacce Turkiyya, Masar, da Qatar suka shiga tsakani tare da goyon bayan Amurka, ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba don kawo karshen hare-haren Isra’ila na shekaru biyu da suka kashe mutane sama da 70,000, galibi mata da yara, tare da jikkata sama da 170,000 tun daga watan Oktoban 2023.