Firaministan Senegal, ya yi kira ga kasashen musulmi da su kaurace wa gwamnatin Isra’ila tare da kara matsa kaimi na mayar da gwamnatin yahudawan sahyoniya saniyar ware.
A yayin wani sabon gangamin goyon bayan Falasdinawa a birnin Dakar na kasar Senegal, ne firaministan kasar Ousmane Sonko ya bayyana hakan.
Wannan shi ne karo na farko tun soma yakin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, da wani babban jami’in kasar Senegal ya halarci zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a Dakar babban birnin kasar Senegal.
“Kauracewa Isra’ila,” “Yancin Gaza,” “Netanyahu mai aikata muggan laifuka”,” na daga cikin taken da masu zanga-zangar suka rera a lokacin tattakin.
Da yake jawabi a wajen gangamin firaministan Senegal, ya yi kira da a kara ba da hadin kai a tsakanin kasashen musulmi don tallafawa Falasdinu.
Ya kuma ce: “Dole ne mu yi kokarin ganin an samar da mafita ta siyasa wacce ita ce mafita ta mayar da kasar Isra’ila saniyar ware”.
“Dole ne a kakaba takunkumin tattalin arziki, siyasa da diflomasiyya kan Isra’ila, inji firaministan na Senegal Usman Sonko.