Kasar Afrika ta Kudu, ta yi Allah wadai da yadda ta ce Isra’ila ke amfani da yunwa a matsayin makamin yaki a Gaza ta hanyar toshe agajin jin kai ga Zirin tun ranar Lahadi.
Isra’ila na “amfani da yunwa a matsayin makamin yaki” a Gaza ta hanyar toshe inji Afirka ta Kudu a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fiyar yau Laraba 5.
“Ta hanyar hana shigowar abinci a Gaza, Isra’ila na ci gaba da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,” in ji Pretoria, wacce dama tun tuni ta shigar da korafi kan Isra’ila akan kisan kiyashi a Gaza a gaban kotun duniya.
Afirka ta Kudu ita ce kasa ta baya-bayan nan da ta yi Allah-wadai da Isra’ila kan katse taimakon ga Gaza, wanda ta ce wata karin shaida ce ta cewa tana amfani da “yunwa” kan Falasdinawa.
A cikin sanarwa da ta fitar, “Afrika ta Kudu ta yi kakkausar suka kan kin amincewar da Isra’ila ta yi na ba da izinin shigar da agajin jin kai a zirin Gaza da kuma rufe mashigar kan iyakokinta a daidai lokacin da al’ummar Gaza ke fama da wahalhalu masu yawa da kuma bukatar abinci da matsuguni da magunguna cikin gaggawa.”
Idan ana tune a watan Janairun 2024, Afirka ta Kudu ta gabatar da karar kisan kare dangi a kan Isra’ila a gaban kotun ICJ.