Gaza: Adadin Wadanda Sukayi Shahada Sanadin Hare-haren Isra’ila Ya Kai 44,382

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da shahadar mutane 44,382 a zirin Gaza a tsawon kwanaki 421 na hare-haren Isra’ila kan  zirin da aka yi

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da shahadar mutane 44,382 a zirin Gaza a tsawon kwanaki 421 na hare-haren Isra’ila kan  zirin da aka yi wa kawanya.

A cikin sanarwar da ma’aikatar lafiyar ta bayyana cewa : A cikin sa’o’i 24 da suka gabata sojojin yahudawan sahyoniya sun aikata laifuka hudu a zirin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa 19 tare da jikkata wasu 72 na daban. »

Baya ga wadanda sukayi shahada akwai wasu 105,142 wadanda galibinsu mata ne da kananan yara da suka jikkata inji sanarwar.

Haka ma halin jin kai a zirin Gaza ya yi muni, wanda ya hadasssa matsananciyar yunwa da wahala.

Hukumomin Gaza sun yi kakkausar suka kan gazawar kungiyoyin jin kai wajen daukar matakan gaggawa ga al’ummar Gaza.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana matukar damuwarsa kan hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kaiwa asibitoci a zirin Gaza.

Hare-haren na barazana ga rayuwar jarirai inda asusun ya bukaci a gaggauta kawo karshen yakin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments