A rana ta 302 na kisan kiyashi da Isra’ila take aiwatarwa a zirin Gaza, sojojin mamaya na Isra’ila sun yi kisan kiyashi guda uku kan al’ummar Falasdinu, inda suka kashe mutane 31 tare da jikkata wasu 62 cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Wannan ya sanya adadin Falasdinawa da suka kashe tun daga farkon hare-haren da Isra’ila Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba zuwa yanzu ya kai mutane 39,550, baya ga jikkata 91,280, a cewar rahoton kullum da ma’aikatar lafiya ta Gaza ta fitar.
Yawan wadanda abin ya shafa na makale a karkashin baraguzan ginin, yayin da kungiyoyin agaji suka kasa kai musu dauki.
A wani labarin kuma, Hukumar tsaron farar hula ta Gaza ta bayar da rahoton cewa, sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun rusa tare da jefa bama-bamai a gine-gine a kwalejin jami’ar da ke unguwar Tal al-Hawa a kudu maso yammacin birnin Gaza.
A garin Khan Younis, dakarun farar hula sun yi nasarar gano gawarwakin shahidai biyu kusa da al-Amir Chalet a garin al-Qarara dake gabashin birnin Khan Younis.
Bugu da kari, wani harin da Isra’ila ta kai ta sama a kusa da filin wasa na al-jazeera da ke birnin Gaza, lamarin ya haifar da karuwar barna a yankin.
A gefe guda kuma, an sake yin wani kisan kiyashi a kudancin zirin Gaza yayin da mutane biyar suka yi shhada kana wasu uku suka bace bayan wani harin bam da Isra’ila ta kai kan wani gida a yankin Miraj da ke kudancin birnin Khan Younis.