Gagarumar Zanga-Zangar Ashura Da Goyon Bayan Al’ummar Falasdinu A Birnin Landon

Al’ummar Birtaniya sun gudanar da gagarumar zanga-zangar tunawa da Ashura a birnin Landan tare da nuna goyon baya ga Gaza Al’ummar Musulmi a birnin Landan

Al’ummar Birtaniya sun gudanar da gagarumar zanga-zangar tunawa da Ashura a birnin Landan tare da nuna goyon baya ga Gaza

Al’ummar Musulmi a birnin Landan na kasar Birtaniya, daga sassa daban-daban na Masarautar sun gudanar da zanga-zangar juyayin Ashura, inda suka gudanar da wani gagarumin tattaki domin jaddada juyayinsu da kisan gillar da aka yi wa Imam Husaini (a.s) da iyalan gidansa gami da sahabbansa a ranar 10 ga watan Muharram a filin Karbala. Wannan tattakin dai ya zo daidai da kisa da ke ci gaba da y ikan al’ummar Gaza, wanda suka bayyana a matsayin “Karbala na wannan zamani.

A kowace shekara al’ummar musulmi a fadin duniya suna gudanar da taron yuyayin Ashura domin nuna alhininsu kan kisan gillar da aka yi wa Imam Husain {a.s} a ranar Ashura, tare da tunawa da sadaukarwar da Imam Husaini (a.s) ya yi a Karbala.

A wannan shekara, birnin Landan ya fuskanci gagarumin jerin gwano mai taken “Raya juyayin Ashura, da jaddada goyon bayan Gaza,” inda mahalarta taron suka nuna goyon bayansu ga al’ummar Gaza da suke fuskantar kisan gilla da kawanya dakuma hare-haren wuce gona da iri.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments