Shugaban kasar ta Iran ya yi tsokaci akan yarjejeniyar da aka rattaba hannu akanta a tsakanin Iran da Rasha a jiya Juma’a, yana mai kara da cewa; Za ta sa abokan gaba masu hargitsa zaman lafiya su yanke kauna.
A jiya juma’a ne dai shugaban kasar ta Iran ta yi wani zaman tattaunawa da ‘yan kasuwar kasar Rasha, a birnin Moscow inda ya kara da cewa; Wannan yarjejeniyar mai muhimmanci tana a matsayin wata taswirar aiki ce da kasashen biyu za su rika bi ta kanta sannu a hankali.
Haka nan kuma ya kara da cewa azama da kudurin da gwamnatocin biyu masu makwabtaka da juna suke da shi ne ya share hanyar kai wa ga rattaba hannu akan wanann yarjejeniyar.
Shugaban na kasar Iran ya fadawa ‘yan kasuwar na Rasha cewa cin moriyar da kasashen biyu za su yi da damammakin da suke da su yana da bukatuwa da kafa kwamitocin na ttatalin arziki da kuma kasuwanci.
Har ila yau shugaba Mas’ud Fizishkiyan ya ce, gwamnatin Iran tana cikin shirin saukake wa ‘yan kasuwar Rasha hanyoyin zuba hannun jari a cikin Iran, domin aiwatar da kasuwanci a tsakanin kasashen biyu ba tare da matsala ba.