Shugaban kasar Iran wanda ya tattauna ta wayar tarho da sarkin kasar Oman, ya bayyana cewa; Idan kan al’ummar musulmi a hade yake, to HKI ba ta isa ta aikata wadannan laifukan da take yi ba.
Shugaban kasar ta Iran ya kuma jinjinawa kasar ta Oman akan matsayarta ta kin amincewa da laifukan da HKI take tafkawa a Gaza da kuma Lebanon.
A nashi gefen, sarkin Oman Sultan Haitham Bin Tariq Sa’id, ya bayyana cewa kare hakkokin Falasdinawa da Lebanon suna cikin batutuwa masu muhimmanci a gaban kasarsa. Har ila yau ya yi tir da yadda kasashen turai suke cigaba da goyon bayan HKI akan laifukan da take aikatawa.
Har ila yau bangarorin biyu sun tattauna akan hanyoyin bunkasa alakar kasashen biyu ta fuskoki daban-daban.