Fiye Da Mutane  300 Ne Su Ka Yi Shahada A Kudancin Lebanon A Yau Litinin

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, sanadiyyar hare-haren ta’addancin HKI a kasar Lebanon, adadin mutanen da su ka yi shahada sun

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, sanadiyyar hare-haren ta’addancin HKI a kasar Lebanon, adadin mutanen da su ka yi shahada sun kai 274  yayin wadanda su ka jikkata su ka kai 10,24.

HKI ta kai hare-haren ne a cikin garuruwa da kauyuka mabanbanta na kudancin Lebanon da kuma gabashinta da kuma yankin al-tuffah.

Hare-haren sun shafi garuruwan Nabadiyyah, Zahrani da Biqa’ul-Garbi. Haka nan kuma jiragen yakin HKI sun kai wasu hare-haren akan yankunan Saida, da Biqaul-Sharqi, sai Hirmil.

Motocin daukar marasa lafiya sun riga zarya akan titunan garuruwan da aka kai wa hare-haren domin daukar gawawwaki da kuma wadanda su ka jikkata.

HKI ta yi amfani da jiragen sama ne wajen kai hare-haren, haka nan kuma manyan bindigogi.

A nata gefen kungiyar Hizbullah ta sanar da kai hare-haren mayar da martani ta hanyar harba rokoki da makamai masu linzami akan sansanonin soja da kamfanonin kera makaman yaki na HKI. Garuruwan da hare-haren kungiyar ta Hizbullah ya shafa sun hada da Safad, Nahariya, Haifa da Nasirah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments