Fiye Da Mutane 20 Ne Su Ka Yi Shahada Sanadiyyar Hare-haren  Amurka Da Birtaniya Akan Kasar Yemen

Da safiyar yau Lahadi, sojojin Amurka da Birtaniya sun ci gaba da kai wa kasar Yemen hare-hare, inda a bayan nan su kai wasu jerin

Da safiyar yau Lahadi, sojojin Amurka da Birtaniya sun ci gaba da kai wa kasar Yemen hare-hare, inda a bayan nan su kai wasu jerin hare-hare guda uku.

Yankunan da hare-haren na Amurka da Birtaniya su ka shafa a cikin Yemen sun hada “ali Sabba”, dake gundumar Sahhar, da hakan ya yi sanadiyyar kashe daruruwan dabbobi.

Haka nan kuma sojojin na Amurka sun kai wasu hare-haren a gabashin Majzar, dake gundunar “Ma’arib”.

Tun da marecen Asabar ne dai sojojin na Amurka su ka shelanta kai wa Yemen hare-hare a biranen San’aa,Sa’adah, da Zammar.

A birnin Sa’adah, kananan yara 4 sun yi shahada sai kuma wata mace, yayin da wasu mutane fiye da 10 su ka jikkata.

Wasu yankunan da hare-haren na Amurka su ka shafa sun hada da  yankunan Mikra da kuraishiyya a gundumar Baidha’a.

A yankin Jarf, dake birnin San’aa mutane 9 ne su ka yi shahada.

Tashar talabijin din ‘almasirah’ ta kasar Yemen ta bayar da labarin dake cewa jumillar wadanda su ka yi shahada sun kai 24, 14 daga cikinsu a birnin Sanaa,sai kuma  10 a Sa’adah. Haka nan wani adadin da ya kai  23 sun jikkata.

Kungiyar Ansarullah ta Yemen ta jaddada ci gaba  da kai wa jiragen ruwan HKI hare-hare a ruwan “Red sea” har zuwa lokacind a za a kawo karshen hana shigar da kayan agaji ga mutanen Gaza masu azumin Ramadan.

Daga marecen jiya Asabar zuwa tsakar dare, sau 30 Amurka da Birntaniyan su ka kai wa Yemen hare-hare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments