Shugaban ofishin yada labarai a Gaza Salama Marouf, ya yi Allah wadai da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, saboda kin janyewa daga yankin Salahul Din a kudancin Gaza da kuma ci gaba da kutsawa da da kai hare-hare a cikin Rafah.
Marouf ya yi gargadin cewa wadannan ayyuka na nuni da irin mummunan nufi da haramtacciyar kasar Isra’ila ke da shi da kuma yadda take ci gaba da aikata laifuffuka kan al’ummar Palasdinu.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Marouf ya bayyana cewa, a cikin kwanaki goman da suka gabata, sojojin Isra’ila sun kara zafafa hare-hare, duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Ya yi nuni da lamari na baya-bayan nan a matsayin shaida na rashin mutunta yarjejeniyar da Isra’ila ta yi, inda ya ba da rahoton cewa an kashe Falasdinawa biyar da suka hada da ‘yan’uwa biyu a kusa da Roundabout na Kuwait a wani harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai a jiya a yankin Rafah.
Wannan laifi dai ya sanya adadin Falasdinawa da aka kashe tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu zuwa mutane 137, inda aka kashe kusan mutane 52 daga cikinsu a Rafah kadai.
Marouf ya yi watsi da ikirarin Isra’ila da ke cewa mayakan Hamas ne ta kaiwa hari, yana mai tabbatar da cewa, a wadannan hare-hare wadanda aka kashe sun sun hada da mata da kananan yara.