Firay ministan kasar Iraki Mohammed Shia’ al-Sudani a cikin wata hiran da ta hada shi da tshar talabijin ta BBC a birnin London ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar Siriya Bashar Al-Asad ne ya gayyana JMI don ta taimaka mata wajen yakar yan ta’adda ta kungiyar ISIS wadanda suka mamaye kasar a shekara 2014.
Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Assudani yana cewa samuwar kasar Iran a kasar Siriya tun wancan lokacin bisa bukatar halattaciyar gwamnatin kasar Siriya ne. Don taimaka mata a cikin harkokin tsaron kasar.
Firay ministan ya bayyana haka ce a jiya Talata a birnin London, ya kuma kara da cewa a fahintarsa bai kamata wata kasar ta shiga cikin al-amuran wata kasa daga cikin kasashen larabawa. Sai tare da amincewar kasar. Assudani ya tabbatar da cewa akwai dangantaka mai karfi tsakanin kasar Iraqi da Iran kuma hakan don amfanin kasashen biyu.